Kuskure Uku Da Dalibai Keyi Gun Cika Jarabawar JAMB

 



Dalibai da dama kan Samu kasun cikin masu aikata kuskure Uku da zamu kawo a kasa yayin da suke cike Jarabawar JAMB, wasu sukan tsinci kansu a cikin duka uku, wasu biyu wasu Kuma daya.


Yayin da wasu daliban Kuma Basu fadawa cikin ko daya daga cikin wadan nan kurakuran, wanda zamu iya cewa sune masu Kashi goma cikin dari.


Wanan wani kalan kuskure ne haka da dalibai keyi gun cika JAMB?


wanan nasan Yana daga cikin tambayoyin da me karatu yakeyi wa kansa a wannan lokaci, don samun amsar tamabayar ga kura kuren kamar haka:


RUBUTA ADIRESHIN EMAIL BA DAIDAI BA


Wanan Yana daga cikin baban kuskure da dalibai kanyi gurin cika Jarabawar JAMB, akasarin dalibai Basu lura sunyi wanan kuskuren sai bayan sun fara cika gurbin POST UTME, wasu Kuma gurin amincewa da gurbin karatu a shafin CAP.


Abubuwan da suke hadasa wanan kuskure: daukin rijistan Jarabawar da rashin na tsuwa ko gaggawa sabida layin da ake Samu a guraren Rijista JAMB din.


Hanyar kaucewa wanan kuskure: shine samuna natsuwa da Kuma kalon abinda ake cika maka yayin Rijista.


MATSALAR HADAKAR KWASAKWASAI


Wanan shima yana daga cikin kuskure da dalibai kanyi, burin dalibi kawai yaci Jarabawar JAMB hakan yake sa shi ya zabi kwasakwasan da ya kware sosai akan su a matsayin Wanda yake neman gurbin karatun da basu Dace da Hadakar ba.

Dalibai bai gane ya tafka wanna kuskuren har sai ya Samu gurbin karatu ya je tantancewa a jami'ar da yasamu, inda ana kodai su canza Masa ko suna shi gurbin gaba daya.


Abubuwan dake hadasa wanan kuskure: shine rashin tamabayar domin wayar dakai akan sha'anin Bangaren da akeson karanta.


Hanyar kaucewa wanan kuskure: mafi sauki ka tambaya wanda suke karanta Bangaren da kake son karanta su saka alayi, ko Kuma ka ziyarci shafin makarantar dakake so kayi bin cike.


MATSALAR NAMBAR WAYA


Dalibai da dama na ganin wanan ba matsala bace don nayi amfani da layin wani, mafi Muni shine yin amfani da layin masu yin rijista ko wani da aka hadu dashi a gun.


Abubuwan dake hadasa wanan kuskure: rashin tura neman lambar Rijista  da wuri, wasu layinka sukan dau kwanaki Basu turo ma mutum ba, sai tsoro kada a rufe rijistan yasa dalibi Yayi da wani.


Hanayar kauce wa wanan kuskuren: shine kokarin tura sakon da wuri dayin rijistan da wuri da zarar anfara.

tsoffin labarai Sabbin Labarai