Hanyoyin Da Zakabi Gurin Samun Verification Code Daga Shafin NYIF

 



National youth Investment Fund (NYIF), wani tsarin ne da Gwamnatin Tarayya ta Samar don ba wa matasa a fadin Nijeriya bashin kudi don habaka ko Kuma Fara Kasuwaci, a  karkashin ofishin Ministan Matasa.

Matasan da suka samu damar cika bashin da dama na fuskatar matsalar rashin samun verification code a adireshin email  dinsu bayan sun kamala yin rejista kamar yadda aka umurce su da suyi ta hanyar tura musu sakon karta kwana ta wayoyin su.

Da dama matasan na cikin damuwa na rashin samun code din, hakan yasa mukayi nazari mukasa mo ma masu wanan matsalar mafita da yadda zasu Samu code din cikin sauki.


Hanyar da Zakubi gun samun verification code  daga shafin NYIF


Da Farko, ka ziyarci shafin bashin a naurar da ake bwrawzin ta chrome.

Kasaka adireshin shafin (www.nyif.nmfb.com.ng), bayan ya bude kaje kada na Kan "LOGIN"

In shima ya budde sai kaje kasa Zaka ga abubuwa kamar haka (NEVER RECEIVED VERIFICATION TOKEN).

Ka danna shi zai Kara Kai ka wani shafi, inda za abukaci kasaka adireshin email, number wayanka ko Kuma BVN dinka, sai kasa email dinka katabatar wanada kayi rejista dashi ne ka danna SEND.

Da zarar kagama haka to zai nuna maka alamun "verification send successful" ma'ana a tura, said ka bada kamar awa 4 sai ka duba adireshin email dinka zakaga sun turama, wani lokaci yakan fi tsawon awa 4.


Kusani: yawan turawar ku yawan verification code din da zasu tura maka, adon haka ake shawarta ku ku tura sau daya kawai sai kujira.




tsoffin labarai Sabbin Labarai