Kasuwanci Ya Kasu Kashi Nawa Ne?

 



Bayan kasamu illimin meye Kasuwanci da amsar Tambayoyi hudun Farko da yakamata Mai shirrin Fara Kasuwanci Yayi wa kansa, to akwai yuwar Kuma kasan Kasuwanci ya kasu Kashi nawane Kuma ya suke.


Yakamata: KA KARANTA MA'ANAR KASUWANCI MAHANGAR DOKAR KASA


Hakikanin gaskiya Kasuwanci sun kasu Zuwa bangarori da dama sai dai a wannan rubutun zamu kawo wasu kadan daga cikin da suka hada da:


KASUWANCI MUTUM DAYA


wanan wani nau'in Kasuwanci ne da ya kunsa mutum daya ne kachal, shi ke da Alhakin Kula da Kasuwanci sa shi kadai missali: Mai shayi, provision, Mai sayirda lemun Zaki da sauransu .

Samar da kayayeki da Kula da sha'anin gudanar da Kasuwanci kamadaga ingantashi ko habaka shi ya ta'alaka ne a wiyar maishi.

A wannan zamani anfi samun wanan tsarin a aikace a tsakanin al'umma bakidaya.


KASUWANCIN HADAKA


Wanan wani nauyin Kasuwanci ne da yashafi mutum 2 Zuwa sama, ama akasa irin Nijeriya akwai adadin mutane da akayarda su hadu su Samar da kallan wanan Kasuwanci, in suka wuce haka saidai su maida shi kamfani.

Wanan nau'in Kasuwanci akwai Takarda Yarjejiniya a tsakanin dukan Wanda suka yarda su hadu don wanan Kasuwanci.

 Sanan adayan bangare akwai Hadakar kasuwanci na wani lokaci Kan kani shi bai bukatar a rubuta Yarjejiniyar a rubuce sai da fada ta fatar baki.

Dukan hakin Kula da wanan tsarin Kasuwanci ya a rubuce ne acikin takardan Yarjejiniyar, Kama daga albashi, raba riba ko faduwa tsakanin kowa ne manba.


KASUWANCI WANI CIBIYA/KUNGIYA GUDA


Wanan wani kalan Kasuwanci ne da akeyi a cikin kungiyoyi/cibiyoyi,  inda dukan mambibin kungiyar  ne ka iya siya kayayyakin da ake siyarwa.

 Domin da kudin kungiyar ake siyo kayan donyin ragome ga Membobi nawaje bazai iya siya daga cikin wanan Kasuwanci ba.


KASUWANCI KAMFANI


Wanan Kasuwanci ne dake bukatar masu zuba hannun jari don gudanar dashi, inda Mai kamfani daban masu zuba hanu jari a ciki daban, sanan alhakin yanke shawarwarin inganta tsarin Kasuwanci ya ta'alaka ne a wuyan su duka.


KASUWANCI BA DON RIBA BAH


Wanan ni tsarin Kasuwanci ne da akeyi ba don riba bah saidai don Taimakon al'umma da kungiyoyi masu zaman kansu keyi.

Wanan kalan Kasuwanci Yana kamance ceniyi da Kasuwanci cibiya guda ama sun Sha ban ban.

Don achan yamkungiya ne ke Moran Kasuwanci ama anan Jama'a garine ke mora domin ko kyauta suke raba kayayakin ga al'umma.



Wadanan na daga cikin kalloli kadan da zamu iya kawo muku a halin yanzu






tsoffin labarai Sabbin Labarai