Menene Kasuwanci?


 


Kalmar Kasuwanci ba bakuwar kalma bace ko sabuwa, kalmace da aka dade ana amfani da ita a tarihin duniya baki daya.


Kalmar Tana da ma'anoni da dama yadanganta da yada kowa yake amfani da ita, a wanen bangare zamu kawo ma'anoni Uku da aka fi lakaba mata:


Ma'ana tafarko:


Kalmar Kasuwanci Na nufin wata masana'anta. Misali Masana'antar hada takalmi, huluna, lemu da sauransu su.


Ma'ana tabiyu:


Kalmar Kasuwanci Na nufin Samar da kayayeki da Jama'a suke bukata  don amfani su na yau da kulum Wanda babu akusa da su. Misali kamar masu shaguna provision.


Ma'ana ta Uku:


Kalmar na iya daukar ma'anar  bangare guda na wata fan'ni. Misali fan'nin noma, ciwo da sauransu.


Wadanan kadan daga cikin ma'anonin Kasuwanci ke nan. 


Dubba  da ma'anonin da muka kawo a sama, mutum zai iya cewa kalmar Kasuwanci ya shafi Samar da abubuwa da Jama'a ke bukata a  yankunan su Wanda babu su akusa sanan ana bukatar su dole.


Duk wanda ke bukatar Fara Kasuwanci, dole ne ya sa'aransa cewa yanaso ne yasamar wada jama'ar sa mafita, ta matsalar saukin samun wasu abubuwa da suke bukata na yau da kulum, Kamar yadda kowane yankuna keda bukatar abubuwa dabban dabban ama Basu Samu su sai a nesa.


Kafin fara Kasuwanci akwai tamboyi da yakamata kowa ya makan sa kamar haka.



 1.  Mene ne ake bukata a yanki  danake zaune?

 2. Ya za'ayi nasamo abin nakawo sa yankina?

 3. A ina Zan sameshi afarashi Mai arha da inganci?

 4. Ina kowasa nawa yakamata na siyar dashi?

 

Amsoshin wanan tamboyoyi Yana atatare da Matakin farko Na Fara Kasuwanci acikin zuciyoyin Wanda ke bukatar Fara Kasuwanci.



tsoffin labarai Sabbin Labarai