Amsoshin Tambayoyi hudu, Farko n Fara Kasuwanci

 



Bayan sannin ma'anar Kasuwanci, akwai wasu Tambayoyi da yakamata duk wanda ke son Fara Kasuwanci Yayi wa kansa.


Yakamata: ka Danna nan Don karanta ma'anar Kasuwanci


A wannan rubutu zaku samu  amsoshin tamboyoyi hudu Na farkon Fara Kasuwanci da wanda me bukatar farawa ya kamata Yayi wa kansa, tambayoyin sun hada da:


TAMBAYAR FARKO: Mene ne ake bukata a yanki  danake zaune?


AMSA:


Tambayar da kowani Sabon Dan Kasuwa yakama ta Yayi wakansa kenan, anan ana bukatar mutum Yayi nazari gaske don gano meye yankisa suke da bukata Wanda sai anje guri me nisan gaske ake samunsa?. 

Zai iya hadawa da tambayar abokansa ko makwabtan sa cikin siyaya da hikma ( missali, wanne akaf unguwan nan ai abukaza yafi kowane abukaza wahalar Samu Kuma gashi ana da bukatar sa), ka tabatar abinda akafi Samu Zaka fada cewa shi ne mafi wahala, nan take zakaji sun fara kirga maka abubuwa da ke da wahalar Samu.

Bayan kasamu sai kazabi Wanda kake da Ra'ayi akansa.


TAMBAYA TA BIYU: Ya za'ayi nasamo abin nakawo sa yankina?


AMSA:


Anan Zakayi bincike ne na inda ake samun abun da ake bukatar a yankin naka.

Binciken ka kada ya tsaya a guri daya yazama akala gurare kada Yayi kasa da 5 mafi karanci.

Kusani: Bincike na da matukar tasiri a  Fara Kasuwanci, ko gun habaka sa.


 TAMBAYA TA UKU: A ina Zan sameshi afarashi Mai arha da inganci?


AMSA:


Bayan kasamu amsar tambaya ta biyu, anan zakaduba dukan guraren da kasamu, anawa ne suke siyar wa dole sai kasamu inda daya yafi Daya tsada ko harha Sanan indayafi inganci.

Anan sai katantance inane acikin su duka yafi arha Kuma da inganci   me kyau, sai yazama zabin ka gun siyan kayayeki.


TAMBAYA TA HUDU: Ina kowasa nawa yakamata na siyar dashi?


AMSA:


Anan ne mafi yawan Yan kasuwa ke Samu matsaloli da dama sabida kowa burinsa inya kawo kaya ya siyar da yaci riba dayawa, mu tuna da wani dabara da masana tatalin suke fada "Yawan arha kaya yawan masu siyansa yawan tsadan sa karanci masu siyansa".

Dole ne kaduba nawa suke fita susiyo shi a wanjen unguwa sanan nawa Kai kayan ya tashin ma har zuwa yankin?. 

Daganan sai ka yenke shawara nawa yakamata kasiyar, inso samu ne kada kasa farashin shi ya wuce yada suke siya a waje, kodai kabarshi afarashin ko kuma yayi kasa Koda da ragin naira biyar ne.


Dazarar kagama amsa wadanan Tambayoyi to ka Kama hanyar Fara Kasuwanci.

tsoffin labarai Sabbin Labarai