Kowace kasa nada nata dokoki da ta tsara a fanin sha'anin gudanar Kasuwanci acikin kasarta Wanda yasha banban da kowane kasa.
Adon haka muka zakulo mafi mahimmanci daga cikin dokoki da kowace kasa ta tanadar wa duk wanda yake son kasuwanci a fadin kasar.
Kasuwanci a Manhagar doka, shine Kula Yarjejiniya tsakanin mutane guda biyu ko sama da haka (Mai siya da me siyarwa), da zumar musayan abubuwan bukatu.
Bukatar me siyar wa kudi ko Abu me darajar kudi, shi Kuma me siya abun da yake bukata ko Dan tafiyar da harkokin yauda kulum ko Kuma bukatan cikin gida.
SHARUDAN DA DOLE SAI ANKIYAYE TSAKANIN ME SIYA DA MESIYARWA
YAKAMATA KU DANA NAN DON KARANTA AMSOSHI HUDUN FARKON FARA KASUWANCI
1. DOLE NE KAYAN DA ZAKA SIYA KO SIYARWA YAZAMA DOKA TA YARDA DASHI
Anan ana nufi dole ne yazama kayan ka yazama Yana cikin kayeyakin da dokokin kasa ta yarda a siya da siyar da su a fadin kasa. Domin akwai haramtatun kayeyakin da doka ta haramta.
Sanan dole yazama kayan nada darajar kudi.
2. DOLE MESIYE/SIYARWA YAZAMA MAI CIKAKEN HANKALI
Anan ana nufin Dole sai kowane yatabatar da zai siyar da ko Zaka siya abu a hannu me cikaken hankali.
Donko ba ayarjejeniya da Wanda bashi da hanakali (mahaukaci, ko Wanda yasha abin da ya gusar Masa da hankalin sa).
Wadanan nadaga cikin abubuwa da dokokin suka yarda dashi gun kulla Kasuwanci.
