Abubuwa Biyar Dalibai Zasuyi Don Samun Gurbin karatun A Jami'oin Nijeriya

 



Samun gurbin karatu abune Mai matukar sauki indan dalibai sun kiyaye wadanan matakan guda biyar da zamu zayyana.


Dalibai da dama na rasa gurbin karatune in basu cika wadanan sharadu ba, hakan yake haifar musu da tuninin cewa don basu San kowa bane a Jami'ar da suke nema, wanda hakan ba daidai bane.


Abubuwa biyar da dalibi zaiyi yasamu gurbin karatu a jami'a:


KARANTA: KUSKURE UKU DA DALIBAI KEYI GUN CIKA JAMB



 1.  KATABATAR KACI JAMB

 

Abu na farko da dalibi zaiyi shine ya tabatar ya ci jarabawar JAMB, wato Makin sa ya kai adadin da ake bukata ko ma yafi.

Wanan shine matakin farko na samun gurbin karatu.


 2. KATABATAR HADAKAR DARUSAN KA SUNYI DAIDAI DAYADA AKE BUKATA


Wanan na daya daga kuskure da dalibai Kan tafka gun cika jarabawar JAMB, a don haka in kanason samun gurbin karatu, to Dole sai ka kiyaye wanan mataki karanta Karin bayanan Kan kuskure da Zaka kiyaye. DANA NAN DON SANNI SU


 3. KA DAURA SAKAMAKON OLEVEL DINKA A SHAFIN JAMB


Dole ne katabatar kaje an daura maka sakamakon Olevel dinka(WAEC,NECO,NEBTEB ko NBAIS), a shafin Jamb. Anso kadaura tun kafin lokacin da za afara sakin gurbin karatu a shafin JAMB din.



 4.  KACIKA GURBIN POST UTME JAMI'AR DAKAKE NEMA


da dama mutane kanki cikawa sabida suna da tuninin da kaci JAMB shikenan zaka samun gurbin karatu, wanan ba gaskiya bane Dole sai kecika gurbin post UTME sanan zaka Samu  damar samun gurbin karatu a jami'ar Nijeriya.

Waso Jami'oin ma sai kunyi jarabawa wasu Kuma ba sai kunyi ba.


 5.  KA AMINCE DA GURBIN KARATU A SHAFIN JAMB


Dole kadinga ziyarta shafin JAMB CAPs akai akai don amincewa da gurbin karatu da aka baka, rashin yin hakan ne zai sa Hukumar JAMB su kwace gurbin subawa wani adon haka kakasance mai ziyarta shafin a kullun.


Duk dalibin Daya cika wanan matakan biyar, Yana da garanti samun gurbin karatu a fadin Jami'oin dake Nijeriya.

tsoffin labarai Sabbin Labarai